29 Satumba 2020 - 12:21
Zarif: Amurkawa Matsorata Ne Masu Halayyar Namun Daji

Ministan harkokin wajen na Iran Dr. Muhammad Jawad Zarif ya yi ishara da kisan gillar da Amurka ta yi wa Birgediya janar Shahid Kassim Sulaimani wanda shi ne ya murkushe kungiyar ‘yan ta’adda ta Da’esh, sannan ya kara da cewa:

ABNA24 : Amurkawa matsorata ne, kuma masu halayya irin ta namun daji, amma duk da haka ba za su iya durkusar da al’ummar Iran ba.”

Muhammad Jawad Zarif ya gabatar da jawabi ne a yau Litinin da ake tunawa da ranar girmama shahidan ma’aikatar waje, a karkashin makon tsaron kasa mai tsarki da Iraki ta kallafawa Iran yaki.

Ministan harkokin wajen na Iran ya jinjinawa shahidan juyin juya halin musulunci na Iran da na lokacin tsaron kasa mai tsarki da wadanda su ka yi shahada a fagen kare shirin makaman Nukiliyar Iran da masu kare hubbarorin iyalan manzon Allah (a.s.w.)

342/